Tinubu ya amince da naɗin Mahmud Yakubu a matsayin jakadan Najeriya a Qatar, Fani-Kayode a Jamus, tare da wasu 63

Bola Tinubu Bola 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin jakadu 65 da za su wakilci Najeriya a ofisoshin jakadancin ƙasar a ƙasashen waje da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.

Jakadun sun haɗa da mutum 31 waɗanda ba jami’an ma’aikatar harkokin waje ba ne da kuma mutum 34 da suka kasance ƙwararrun jami’an diflomasiyya, waɗanda Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗinsu a watan Disamba na shekarar 2025.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar.

Daga cikin waɗanda ba ƙwararrun jami’an diflomasiyya ba akwai tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode wanda aka tura Jamus, yayin da Jimoh Ibrahim aka naɗa wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Reno Omokri an tura shi ƙasar Mexico, yayin da Lateef Are zai yi aiki a matsayin jakadan Najeriya a Amurka.

Tsohon ministan lafiya Isaac Adewole an tura shi ƙasar Canada, yayin da Aminu Dalhatu zai yi aiki a matsayin babban kwamishina a ƙasar Birtaniya.

Sauran waɗanda ba ƙwararrun jami’an diflomasiyya ba sun haɗa da Ita Enang zuwa Afirka ta Kudu, tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mahmood Yakubu zuwa Qatar da kuma Grace Bent zuwa Togo.

Daga cikin ƙwararrun jami’an diflomasiyya kuma, Mohammed Mahmud Lele an tura shi Algeria, Shehu Barde zuwa Ghana, yayin da Abdussalam Zayyad zai yi aiki a Senegal.

Sauran sun haɗa da Bako Umar zuwa Morocco, Aminu Nasir zuwa Habasha da Ibrahim Danlami zuwa Kenya.

Onanuga ya bayyana cewa Ma’aikatar Harkokin Waje ta riga ta samu amincewar ƙasar Birtaniya ga Aminu Dalhatu da kuma amincewar Faransa ga Ayodele Oke.

Ya ƙara da cewa an miƙa sunayen sauran jakadun ga ƙasashen da za su karɓe su domin samun amincewa kamar yadda dokokin diflomasiyya suka tanada.

Shugaban ƙasar ya kuma umarci Ma’aikatar Harkokin Waje da ta fara shirin horaswa ga waɗanda aka naɗa a matsayin jakadu da manyan kwamishinoni nan take.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa jerin sunayen jakadun sun haɗa da mutane da dama da aka tura ƙasashe daban-daban na duniya domin wakiltar Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here