Shugaba Buhari ya ɗage dakatar da ayyukan Twitter

twitter image
twitter image

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince da ɗage haramcin yin amfani da kafar sada zumunta ta Twitter.

Shugaban ƙasar ya bayyana wannan matsaya ne yau Juma’a a Abuja yayin da yake jawabi ga ƴan ƙasa a jawabin cikar Najeriya shekaru 61 da samun ƴancin kai.

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya a ranar 5 ga Yuni, don ba da damar gwamnati ta dauki matakai don magance kalaman tada tarzoma da ake yaɗawa a dandalin.

Yayin jawabin, shugaba Buhari ya sanarwar cewa Kwamitin Shugaban kasa da ya kafa, tare da Kwamitin Fasaha, don shiga Twitter don bincika yiwuwar warware matsalar da ta haifar da dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya ya samu nasarar magance wasu muhimman batutuwa.

Ya ce, “Bayan dakatar da ayyukan Twitter, Kamfanin na Twitter Inc ya tuntuɓi gwamnatin tarayya don warware matsalar, Bayan haka, na kafa kwamitin Shugaban kasa don shiga Twitter don bincika yiwuwar warware matsalar”.

“Kwamitin, tare da tawagar jami’an Fasaharsa, sun yi aiki tare da Twitter kuma sun magance manyan batutuwa da yawa.

“Bayan dumbin ayyukan da ake yi, ana magance batutuwan kuma na ba da umarnin a dakatar da dakatarwar amma sai idan an cika sharuddan don ba da damar ƴan kasarmu su ci gaba da amfani da dandamali don kasuwanci da kyawawan ayyuka.

Haka nan, Shugaban ya bayyana cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar tabbatar da cewa kamfanonin sadarwar zamani na yin amfani da dandalin su don inganta rayuwar ƴan Najeriya da mutunta ikon kasar da dabi’u da kuma al’adu da inganta amincin yanar gizo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here