PDP ta sauya ranar gudanar da tarukan NEC da BOT

PDP members
PDP members

Jam’iyyar PDP ta kasa za ta sake zama ranar Laraba domin ci gaba da tattaunawa kan jadawalin jam’iyyar na zaben 2023 da sauran muhimman batutuwa.

Sakataren yada labarai na kasa Debo Ologunagba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron majalisar zartaswar jam’iyyar karo na 41 da aka gudanar a daren ranar Litinin a Abuja.

Ya ce yayin da aka dage taron kwamitin gudanarwa na kasa (NEC) da na kwamitin amintattu da aka shirya gudanarwa ranar Talata zuwa ranar laraba, inda za’a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban jam’iyyar.

“Bayan tattaunawa tare da dogon nazari, mun dage taron zuwa ranar Laraba domin ci gaba da duk wasu batutuwan da aka tattauna.

“A ranar Laraba da karfe 10 na safe za a gudanar da taron kwamitin, daga nan kuma za a yi taron BoT sannan kuma taron NEC,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here