NCC ta umarci kamfanoni su riƙa sanarwa kafin samun matsalar Network

ncc new

Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta umurci kamfanonin sadarwar layukan Waya da su riƙa sanar da kwastomominsu duk  lokacin da za a fuskanci katse war yanar sadarwa.

Hukumar ta NCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da mukaddashin jami’arta ta hulda da jama’a Misis Nnenna Ukoha, ta fitar ranar Lahadi.

Umurnin Hukumar ya buƙaci kamfanonin  da su bayar da cikakkun bayanai kan musabbabin katsewar da wuraren da abun ya shafa da kuma kiyasin lokacin da matsalar za ta ɗauka.

Ta ce an dauki matakin ne da nufin inganta amfani da wayoyi ba tare da tangarɗa ba, tare kuma da aikata gaskiya da rikon amana a fannin na sadarwa da kuma tabbatar da cewa an sanar da masu amfani da layukan game da katsewar ayyukan da ka iya shafar bukatun sadarwar su.

Hukumar ta NCC ta kuma ba da umarnin sanar da kwastomomi akalla mako guda kafin duk wata matsala da ta ke shirin faruwa.

Haka kuma ta ƙara da cewa, wannan umarni ya shafi kamfanonin sadarwar wayar hannu, masu ba da sabis na intanet, da kuma kira.

A cewar sanarwar, akwai tanadin biyan diyya matukar katsewar ta kai ta tsawon Sa’o’i 24 ba tare da an shawo kanta ba.

Hukumar ta NCC ta ce: “Mun gano manyan matsaloli guda uku da suka hada da duk wani yanayi na aiki na hanyar sadarwa kamar yanke wayoyin sadarwa sakamakon gini ko matsalar samun damar shiga, ko sata da barna da ke shafar kashi biyar ko fiye na ma’aikatan da abin ya shafa ko kuma kananan hukumomi biyar ko sama da haka.

Da yake tsokaci game da umarnin, Daraktan sashe lura ayyukan kamfanonin da kuma tabbatar da ingancin ayyukansu da na hukumar Mista Edoyemi Ogor, ya ce hukumar ta gwada tsarin bibiya da kuma adana bayanai kan ayyukan kamfanonin sadarwar na wasu watanni gabanin daukar wannan mataki tare da bayar da umarnin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here