Majalisar wakilai ta amince da ƙudirin dokar gyaran Haraji

Reps 750x430

Shugaban kwamitin Kudi na majalisar wakilai, James Faleke na jam’iyyar APC daga jihar Lagos, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, kudirin gyara dokar harajin zai samar da dokoki da za su amince da su.

Faleke ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis bayan majalisar ta yi nazari tare da amincewa da rahotan kudirin gyaran haraji guda hudu a zamanta da ta yi a Abuja.

Kudurorin sun hada da dokar harajin Najeriya, daftarin kula da haraji, da dokar hukumar haraji, da kuma dokar kafa hukumar tattara kudaden shiga ta kasa.

“Wadannan kudurorin an shafe kwanaki uku ana zaman sauraren ra’ayoyin jama’a, tare da gabatar da bayanai daga manyan masu ruwa da tsaki sama da 80. Bayan haka, mun gudanar da hutu na kwanaki takwas don yin muhawara a kowane sashe.

Karanta: Majalisar wakilai za ta fara zaman sauraren ra’ayoyin jama’a game da kudirin gyara haraji

Ya nuna godiya ga ‘yan majalisar da ‘yan Najeriya da suka yi aiki da kudirin, yana mai tabbatar da cewa dokokin da aka fitar za su kasance abin karbuwa ga kowa.

Faleke ya kuma mika godiyarsa ga shugabannin majalisar kan amincewar kwamitinsa wajen gudanar da nazari kan haraji tare da gabatar da su domin tantancewa.

Ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan yadda ya ba da fifiko wajen gyaran dokar haraji, inda ya ce wasu dokokin haraji da ake da su tun daga shekarar 1959 ne.

“Ba za mu iya ci gaba da amfani da tsoffin dokokin haraji waɗanda ba za su iya biyan kasuwancinmu, rayuwa, da buƙatun kudaden shiga ba,” in ji shi.

Mataimakin shugaban kwamitin, Sa’idu Abdullahi na jam’iyyar APC daga jihar Niger, ya ce babu wani kudiri a majalisa ta 10 da ya haifar da mahawara kamar kudirin sake fasalin haraji.

Ya yabawa kakakin majalisar Tajudeen Abbas bisa samar da fahimtar juna a tsakanin masu ruwa da tsaki.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here