Majalisar dattawan Najeriya, ta ce, akwai yiwuwar kara yawan alkalai a kotun koli daga 21 zuwa 30, domin rage yawan shari’u da ke taruwa a gaban kotun da kuma saurin yanke hukunci.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani kudiri da Sanata Osita Izunaso daga mazabar Imo ta yamma ya gabatar, inda ya ce alkalai 21 ba za su wadatar ba, duk da an nada su ne tun a shekarar 2023.
Sanata Izunaso ya ce, adadin alkalai 30 zai ba da damar kafa kwamitoci fiye da hudu a lokaci guda, wanda hakan zai taimaka wajen gudanar da shari’u cikin sauri.
“Alkalan kotun koli yawanci su na zama a cikin bangarori biyar, ko bakwai kamar yadda ya ke a dokance,” in ji shi.
Ya ce, bai kamata a bar shari’o’i kamar rikicin gidan haya ko rashin jituwar iyali a kotun koli ba.
Ya ba da misali da wata shari’ar da ta shafi wadanda suka mutu, da ake jira a saurare su, shekaru uku bayan da iyalai suka warware ta.
Tun da farko, Izunaso ya ce majalisar dattawan ta na yin nazarin kudirin samar da jihar Anim a shiyyar kudu maso gabashi.
Sanatan ya ce kudirin dokar ya tsallake karatu na biyu kuma yanzu haka ya na gaban kwamitin majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulki.












































