Aminu Bala Madobi-Daga Kano
Dan Majalisar tarayya Fatuhu Muhammad, Mamba Mai wakiltar mazabar Daura-Sandamu-Mai aduwa ya fice daga jam’iyyar APC.
Dan Majalisar Muhammad Fatuhu wanda Dan kanwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sanar dayin murabus din sa a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na mazabar Sarkin Yara’ A’ dake Daura.
Dan Majalisar Ya fice daga jam’iyyar ne bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar a hannun Dan takarar da ya lashe zaben fidda gwanin Aminu Jamu.
Acewar sanarwar, daukan matakan ficewar Dan Majalisar ta biyo bayan ganawar da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP sukayi da Dan Majalisar.
“Ina mai sanar da ku cewa na yi murabus daga jam’iyyar APC ba tare da bata lokaci ba.
“A tareda ni akwai takardar rajistar shiga jam’iyyata mai lamba KT/DRA/10/00002 duk ga su na ajiye.
“Yayin da nake gode muku da jam’iyyar da suka ba ni dama na yi wa al’ummar mazabar Daura/ Sandamu/ Mai ‘Aduwa aiki tare da jam’iyyar, Ina muku fatan alheri.”













































