Matukan jirgin Alpha Jet na rundunar sojin saman Najeriya sun tsira a ranar Asabar bayan jirgin da suke gwaji ya yi hatsari a sansanin NAF da ke Kainji, jihar Neja.
Shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci a kafa kwamitin bincike nan take domin gano musabbabin lamarin.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ta bayyana cewa matukan jirgin sun nuna bajinta da ƙwarewa ta musamman, inda suka yi fitar gaggawa bayan jirgin ya samu matsala yayin binciken aikin da ake yi bayan gyara a sansanin NAF da ke Kainji.
Sanarwar ta ce da zarar jirgin ya tashi, sai ya fuskanci gaggawa, abin da ya sa matukan suka dauki mataki cikin sauri da natsuwa.
Sanarwar ta ce, matukan sun yi ƙoƙarin karkatar da jirgin daga wuraren da ake cunkoson jama’a kafin su yi fitar gaggawa cikin kwarewa.
Matukan yanzu haka suna fuskantar binciken lafiya, yayin da shugaba Aneke ya jinjinawa jarumtaka, ladabi da hangen nesa da suka nuna, wanda ya ceci rayuka.
Rundunar sojin sama ta tabbatar wa jama’a da cewa tana da cikakkiyar aniya wajen kiyaye tsaro da bin ka’idojin aiki domin kare rayukan ma’aikata da ’yan kasa baki ɗaya.













































