Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu ta samu nasara kan abokiyar karawarta Angola da ci biyu da ɗaya a wasan farko na rukuni na B a gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2025 da aka buga a filin wasa na Marrakesh.
Ƙungiyar Bafana Bafana ta Kudancin Afirka ce ta fara zura ƙwallo ta hannun Oswin Appollis, sai dai ƙungiyar Palancas Negras ta Angola ta rinjayi wasan a rabin farko, inda ta daidaita wasan bayan matsin lamba mai yawa da ta yi.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, ‘yan wasan Afirka ta Kudu sun ƙara ƙwazo da kuzari, lamarin da ya kai ga samun nasarar da suka dace ta hannun Lyle Foster, wanda ya jefa ƙwallo mai ban sha’awa saura kusan mintuna goma kafin ƙarshen lokaci.
A farkon wasan, ƙungiyoyin biyu sun samu dama-dama, inda babbar damar Angola ta faɗa hannun Fredy a minti na 15, amma mai tsaron ragar Afirka ta Kudu Ronwen Williams ya yi kyakkyawan tsalle ya hana ƙwallon shiga raga.
Kafin tsakiyar rabin farko, Afirka ta Kudu ta samu gaba, bayan Khuliso Mudau ya tura ƙwallo wadda ta faɗa gaban Oswin Appollis, wanda ya samu sarari a cikin akwatin bugun fanareti ya kuma aika ƙwallo ƙasa ta shiga kusurwar raga.
Angola ta ci gaba da neman ramawa, inda Gelson Dala ya kusa daidaita wasan da bugun kai daga bugun kusurwa, amma Williams ya sake hana su samun nasara.
Daga bisani, a minti na 35, Angola ta daidaita wasan bayan Fredy ya buga bugun tazara, Show ya karkatar da ƙwallon da gefen ƙafarsa zuwa raga.
A rabin na biyu, Afirka ta Kudu ta sake nuna rinjaye, duk da cewa an soke ƙwallon da Tshepang Moremi ya ci bayan duba na’urar VAR saboda kwantan ɓauna.
Daga ƙarshe, Lyle Foster ya tabbatar da nasarar ƙasarsa da kyakkyawar harbi daga bakin akwatin fanareti a minti na 79, wanda ya zama ƙwallon nasara, yayin da Angola ta kasa sake dawowa cikin wasan.
Ƙungiyoyin za su koma fili a ranar Juma’a, inda Angola za ta fafata da Zimbabwe, yayin da Afirka ta Kudu za ta kara da Masar a wasanninta na gaba a gasar.













































