Ƙungiya ta bada gudummawar Naira miliyan 500 ga laburaren Obasanjo

324934160 580877387194399 3635636501705828103 n
324934160 580877387194399 3635636501705828103 n
Gidauniyar Future Africa Leaders Foundation, FALF, ta ba da gudummawar Naira miliyan 500 ga ɗakin karatu na tsohon shugaban Najeriya,Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in gudanarwa, COO, Loveworld, Fasto Ifeoma Chiemeka, ya fitar a ranar Talata, FALF kungiya ce ta Chris Oyakhilome Foundation International, COFI.
An bayar da gudummawar ne ga dakin karatu a ranar 3 ga watan Janairu, yayin da Obasanjo kuma ya karbi lambar yabo ta Future Africa ta 2022, wanda aka gudanar a ranar 31 ga Disamba, 2022.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa gidauniyar ta ba wa matasa 10, daga kasashe daban-daban na Afirka kyautar dala dubu 10 kowannensu, sannan wanda ya lashe kyautar tauraro a cikinsu da karin dala 25,000 duk shekara.
Kyautar da aka bayar ita ce ga matasa su tallafa wa ayyukansu na raya Afirka daga yankunansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here