Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce dole ne jam’iyyun siyasar kasar nan da su bayyana ma ta hanyoyin da suka samu kudaden yakin neman zabensu tare da kiyaye ka’idojin kashe kudaden yakin neman zabe da aka kayyade.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wata hira ta musamman da yayi da gidan talabijin na Trust.
An shirya gabatar da hirar ne a tashar talabijin da karfe 7 na yammacin gobe (Litinin).
A cewar Yakubu, akwai iyakoki da dama da aka ware ga daidaikun mutane da za su iya ba da gudummawa don ba da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe, saboda daidaikun mutane ba za su iya ba da gudummawa haka kawai batareda amfani da ka’idojin da aka sanya musu ba.
“Wadannan suna cikin doka kuma dole ne a yi musu biyayya kuma a mutunta su,” in ji Yakubu.
Shugaban hukumar zaben ya nanata cewa jam’iyyu ba za su iya karbar gudunmawar kudade daga Kasashen waje ba, kuma yin karan-tsaye ga tanadin dokar zai janyo fuskantar hukunci.
Da yake magana kan wadanda suka yi rajista a ci gaba da rajistar masu kada kuri’a da aka kammala a kwanakin baya, Yakubu ya ce hukumar ta tattara bayanan kowacce rajista ta hanyar adana bayanai da zai baiwa me zabe damar yin zabe a karkashin doka.
“Ba a ba ‘yan Najeriya damar yin rajista fiye da sau daya ba, don haka wadanda suke yin rajista sama da daya mun cire bayanansu.
Shugaban na INEC, ya kuma ce, la’akari da abubuwan da suka faru a baya, hukumar ta tuntubi Majalisar Dokoki ta kasa don samar da lokacin da ya kamata a yi amfani da kudade da kuma mikawa hukumar gwargwadon iko kafin zabe.
“Don haka, mun gabatar da adadin kudin kasafi kusan N305bn don gudanarwa da aikin zaben,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta tanadi duk wasu tanade-tanaden da suka dace kan samar da tsaro domin tabbatar da cewa jami’an zabe da kayan zabe da kuma masu zabe sun kasance cikin koshin lafiya yayin gudanar da zaben 2023 mai zuwa.











































