Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahamed Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC ranar Litinin a jihar Lagos.

Kassim Shettima, wanda shine zai yiwa Tinubu mataimaki na daya daga cikin wadan da suka hallarci ganawar.

Sauran wadan da suka hallaci taron sun hada da Atiku Bagudu na Kebbi, Bello Matawalle na Zamfara, Nasir El-Rufai Kaduna, Mohammed Badaru Abubakar Jigawa, Abdullahi Ganduje Kano da kuma Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos.













































