Hukumar kiyaye hadura ta amince da a canjawa wasu Jami’ai 46 wuraren aiki

FRSC Oga
FRSC Oga

Shugaban hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta Kasa, Dakta Boboye Oyeyemi, ya amince da sake canjawa mataimakan shugaban hukumar biyar da kwamandoji 41 wuraren aikinsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Bisi Kazeem, ya fitar, ya ce ana sa ran dukkanin manyan jami’an su 46 za su kai rahoton kama aiki ga sabbin rundunoninsu a ranar Litinin, 2 ga watan Mayu, na shekarar 2022.

Sanarwar ta ce, sabon matakin ya biyo bayan amincewar da hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta tarayya ta yi na karin girma ga manyan jami’ai da kuma bukatar dake akwai ta canjawa jami’an wuraren aiki.

“Jami’an da aka canjawa wuraren aiki su ne ACM Chidi B Nkwonta, tsohon kwamandan shiyyar RS6HQ Fatakwal wanda zai karbi mukamin kwamandan Kolejin bada horo ga jami’an hukumar dake Udi a jihar Enugu,” in ji sanarwar.

‘’ACM Chukwuma N. Njoku, wanda yake matsayin kwamandan rundunar dake kula da sashen gudanarwa a hedikwatar hukumar ta tarayya, da a yanzu ya zama shugaban sashen bunkasa sana’o’in dogaro da kai a karkashin Sashen horarwa na hedikwatar hukumar ta tarayya’’.

A cewar sanarwar, ACM Ocheja I Ameh, tsohon kwamandan hukumar a Ekiti, yanzu an tura shi ya zama kwamandan shiyyar Enugu; haka kuma Uchechukwu I. Wihioka yanzu shi ne mataimakin kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Yayin da CC Joel I. Dagwa, magatakardar hukumar mai barin gado, wanda yanzu aka nada a matsayin mataimakin kwamandan hukumar; CC Shamsudeen A. Sale fwc, tsohon kwamandan shiyyar jihar Nasarawa, yanzu shi ne kwamandan hukumar sashen kula da ababen hawa, a Hedikwatar hukumar ta tarayya.

Sanarwar ta kara da cewa an yi canjin wuraren ayyuka ga karin wasu Kwamandojin, har ma Dakta Boboye Oyoyemi ya bukaci dukkan jami’an da su ci gaba da taka muhimmiyar rawa don ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma dake amfani da hanyoyin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here