Gwamnatin Tarayya ta sanya gwajin miyagun kwayoyi ya zama tilas ga daliban sakandare

Tunji Alausa

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabbin matakai masu tsauri domin yakar shan miyagun ƙwayoyi da sauran abubuwan maye a makarantun sakandare, ciki har da gwajin miyagun ƙwayoyi na tilas ga baliban da dakatarwa na dan lokaci ga daliban da suka ci gaba da ta’ammali bayan an yi nasarar gyara su.

A karkashin sabon shirin, duk sabbin daliban da za su shiga sakandare za a yi musu gwajin tabbatar da rashin ta’ammali da miyagun kwayoyi da zaran sun shiga.

Matakan na cikinJagororin Aiwatar da Yaki da Shan Kwayoyi da Abubuwan Maye a Makarantun sakandire a Najeriya.

Jawabim ya zayyana tsarin gaba daya da nufin rage yaduwar shan abubuwan maye tsakanin daliban da kirkirar yanayin karatu mai aminci a makarantu a fadin kasar.

A cewar takardar, an tsara manufofin ne “don kirkirar yanayi mai kyau na koyo da koyarwa a cibiyoyin ta hanyar rage mummunan tasirin shan abubuwan maye ga lafiyar kwakwalwa da karatun daliban.”

Baya ga gwajin farko, ana sa ran makarantu za su gudanar da gwajin miyagun kwayoyi na lokaci-lokaci da ba zato ba tsammani ga sabbin dalibai da tsofaffi akalla sau daya kowace shekarar karatu.

Takardar ta kara da cewa “duk daliban za su yi gwajin miyagun kwayoyi na lokaci-lokaci kamar yadda hukumomin da suka dace suka ba da shawara.”

Ta haramta wa daliban amfani ko mallakar miyagun kwayoyi, abubuwan da doka ta amince da su ko wasu abubuwan maye ba tare da izinin hukumomin makaranta ba, tana mai cewa “an haramta wa duk daliban amfani ko mallakar miyagun kwayoyi, abubuwan da doka ta amincewa da su ko abubuwan maye ba tare da izinin hukumomin makaranta ba.”

Duk da haka, ta bayyana cewa daliban da ke bukatar magungunan da doka ta amince da su saboda rashin lafiya dole ne iyayensu ko masu kula da su bayyana hakan lokacin shiga makaranta.

Manufofin sun kafa tsarin gwaji da daukar matakin a matakai uku ga daliban da gwaji ya nuna suna ta’ammali da kwayoyin.

A cewar jagorar, “makasudin shi ne gano daliban da ke bukatar taimako da habaka yanayin makaranta mai aminci da lafiya.”

Daliban da gwajin suka fadi a karon farko za a samar da hanyoyin shawarwari da magani na farko kamar yadda hukumomin makaranta suka tsara.

Takardar ta bayyana cewa “mutanen da aka gano suna ta’ammali da miyagun kwayoyi za su yi magani na farko, wanda zai hada da shawarwari kamar yadda hukumomin makaranta suka ya dace.”

Wadanda kuma aka gwada a karo na biyu za a mika su ga kwararru domin karin magani da kulawa ta musamman.

Takardar ta kara da cewa “idan aka sake gano dalibin ya ci gaba da ta’ammali da miyagun kwayoyi, za a mika shi ga kwararrun hukumomin makaranta domin ya samu magani da kulawar da yake bukata.”

Ga daliban da suka ci gaba bayan gwaji da magani karo na uku, manufofin sun tanadi a dakatar da su na dan lokaci daga makaranta.

Manufofin sun kuma sanya shawarwari na wajibi kafin da bayan gwaji ga daliban da za a yi wa gwaji.

A cewar takardar, “shawara ta kafin gwaji ita ce jagorancib da ake bayarwa kafin mutum ya yi gwajin tabbatar da rashin ta’ammali da miyagun kwayoyi, manufarta ita ce shirya mutum, bayyana abin da ake tsammani, rage fargaba, karfafa hadin kai da gina amana.”

Ta kara da cewa “shawara ta bayan gwaji na faruwa bayan an fitar da sakamako, ko tabbatacce ne ko mara kyau. Manufarta ita ce taimaka wa mutum ya karbi sakamakon kuma a bashi shi taimakon da ya dace.”

Domin tabbatar da bin doka, ana sa ran kowace makaranta za ta kafa kwamitin ladabtarwa da shugaban makaranta ke jagoranta tare da ayyuka bayyanannu.

Takardar ta kuma umurci cewa abubuwan tashin hankali masu alaka da shan abubuwan maye, ciki har da fada ko jikkata juna, “dole ne a kai rahoto ga jami’an tsaro.”

Ta kuma gargadi cewa daliban da suka ki bin magani ko gyaran da aka tsara za a dakatar da su na dan lokaci daga makaranta “har sai an gano ya samu kwanciyar hankali.”

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara damuwa kan karuwar shan miyagun kwayoyi da abubuwan maye tsakanin matasa a Najeriya, inda masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da lafiya ke gargadi kan tasirinsa ga karatu, ladabtarwa, lafiyar kwakwalwa da tsaro a makarantu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here