Gwamnatin Jihar Kano ta kashe Naira Biliyan 1 wajen gyaran Asibitin Kwararru na Muhammadu Abdullahi Wase, in ji kwamishinan lafiya Abubakar Labaran.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jagorantar Tawagar ‘Yan Jarida ta Fadar Shugaban Kasa da ke rangadin duba ayyukan da aka kammala da masu gudana, ya ce gin in, wanda ke da gadaje 230, ana cikakken gyara domin inganta bayar da hidima.
A cewarsa, asibitin ya kunshi sassa hudu na asali, akwai na haihuwa, likitancin, yara, da tiyata.
Ya ce asibitin bai taba samun kulawar da yake samu a yanzu ba tun lokacin da aka kafa shi a zamanin mulkin mallaka.
“An mayar da shi sabon asibiti gaba daya; ko’ina tsatsaf,” in ji Labaran.
A jawabinsa, kwamishinan ayyuka, Alhaji Marwan Ahmed-Aminu, ya ce za a kammala aikin asibitin cikin watanni biyu masu zuwa.
Ya ce za a samar wa asibitin kayan aiki na zamani idan an kammala aikin gyaran.
Tun da farko, tawagar ta ziyarci Asibitin Asiya Bayero wanda gwamnatin yanzu ta kwato bayan da gwamnatin da ta gabata ta sayar da shi. (NAN)














































