Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a zaɓen shekarar 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance.
A cikin wasiƙar murabus ɗin da ya rubuta ranar 29 ga Maris, 2026, wadda aka aika wa shugaban APC na mazabar Gawuna a ƙaramar hukumar Nassarawa ta Jihar Kano, Gawuna ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka na fita daga jam’iyyar na kansa ne kuma bisa ra’ayinsa.
Ya bayyana a cikin wasiƙar cewa ya ajiye kasancewarsa ɗan jam’iyyar APC daga ranar 29 ga Maris, 2026, inda ya jaddada cewa matakin ya fara aiki daga wannan rana.
Tsohon mataimakin gwamnan ya nuna godiya ga jam’iyyar APC bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta, yana mai cewa ya amfana da dama a tsawon lokacin da ya yi a matsayin ɗan jam’iyyar.
Sai dai bai bayyana matakin siyasar da zai ɗauka na gaba ba bayan ficewarsa daga APC.
Daily Nigerian ta rawaito cewa murabus ɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano, inda manyan ’yan siyasa ke sauya sheƙa domin shirye-shiryen zaɓuɓɓukan da ke tafe.
Majiyoyi na kusa da shi sun bayyana cewa ana sa ran Gawuna zai gana da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a daren ranar Litinin a gidansa da ke Miller Road.










































