Yanzu-yanzu: DSS ta gurfanar da Malami da ɗansa kan mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da tallafawa ta’addanci

Malami Terrorism DSS

Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami, da ɗansa, Abdulaziz, gaban kotun tarayya a Abuja kan tuhuma guda biyar da suka shafi tallafawa ta’addanci da mallakar makamai haram.

A cikin karar da aka shigar gaban Kotun Tarayya, an zargi Malami da kin gurfanar da wasu da ake zargi da tallafawa ta’addanci, waɗanda aka kawo masa yayin da yake rike da mukamin babban lauya na ƙasa AGF kuma Minista na Shari’a.

An kuma zargi Malami da ɗansa da ajiye makamai a gidansu da ke Gesse Phase II, Birnin Kebbi LGA, Jihar Kebbi ba tare da izini na doka ba.

DSS ta ce a cikin tuhuma ta farko, tsohon AGF ya kasance cikin shirin tallafawa ta’addanci, yayin da a tuhumar biyu zuwa biyar, Malami da ɗansa sun aikata laifi na mallakar bindiga kirari Sturm Magnum 17-0101 da harsasai 16 Redstar AAA 5’20 masu rai da harsasai 27 Redstar AAA 5’20 da aka harba, abin da ya saba wa dokar yaƙi ta’addanci (Prevention and Prohibition) Act, ta 2022 da dokar mallakar makamai ta 2004.

Malami da ɗansa sun musanta laifukan lokacin da aka karanta tuhumar a gabansu.

Bayan sun musanta, lauyan ƙara, Calistus Eze, ya roƙi kotu ta tsare su a hannun DSS har zuwa lokacin fara shari’a.

Lauyan kariya, Shuaibu Aruwan (SAN), ya roƙi a ba su belin baki, yana mai cewa an tsare su a hannun DSS fiye da makonni biyu.

Amma Alƙali Joyce Abdulmalik ta ƙi amincewa da roƙon belin baki, ta ce kotu ce mai hurumi, ta umurci lauya ya shigar da roƙon belin baki na hukuma.

Ta kuma umurci a tsare su a hannun DSS har zuwa ranar 20 ga Fabrairu domin fara shari’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here