Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa haɗin gwiwa da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, bayan ziyarar da gwamnan ya kai wa Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar Kano, Ibrahim Bakori, a ofishinsa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce ƙara ƙulla alaƙar da ke tsakanin gwamnatin jihar da rundunar ’yan sanda, tare da ƙarfafa fahimta da haɗin kai a fannin tsaro.
Ya ce, rashin tsaro na daga cikin manyan ƙalubalen da ya tarar tun bayan hawansa mulki, amma ya jaddada cewa an samu gagarumin ci gaba a ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Ibrahim Bakori.
Gwamnan ya ƙara da cewa, jihar Kano mallakin kowa ce, inda ya bukaci ’yan siyasa su daina amfani da bambancin ra’ayi na siyasa wajen lalata tsaro, ya na mai cewa kare rayuka da dukiyoyi bai kamata ya zama abun wasarairai ba.
A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Bakori, ya yaba da ziyarar gwamnan, ya na mai cewa hakan alama ce ta goyon baya da kyakkyawar niyya, tare da tabbatar da cewa rundunar ’yan sanda za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a Kano.













































