Wani jigon APC ya zargi Mai Mala da neman cin hanci daga wajen Ganduje

5A114B8A C8A5 4854 88B0 A8DBA20943B5
5A114B8A C8A5 4854 88B0 A8DBA20943B5

Wani jigo a jam’iyyar APC a Kano, Hassan Alwan ya yi zargin cewa gwamnan jihar Yobe da kuma shugaban riko na jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya bukaci gwamna Abdullahi Ganduje ya ba shi cin hanci.

Alwan ya yi wannan zargin ne yayin da yake bayani a wani shirin gidan Talabijin na Channels mai suna “Sunday Politics” a ranar 20 ga Fabrairu, 2022.

Ya yi wannan tsokaci ne game da rashin gudanar da taron jam’iyyar APC na kasa da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada kwamitin riko da Buni ke jagoranta bayan rusa tsohon shugabancin na kasa karkashin jagorancin Adams Oshiomhole, inda aka dorawa Buni alhakin shirya babban taron jam’iyyar na kasa.

Sai dai kuma a halin yanzu jam’iyyar na cikin rikicin cikin gida da ake zargin cewa bangarori daban-daban na son karbe ikon jam’iyyar gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

An samu bullar bangarori daban-daban a fadin jihohin kasar, musamman a Kano inda Sen. Ibrahim Shekarau da Ganduje ke fafatawa da juna domin ganin jam’iyyar ta samu nasara.

Sai dai a ranar Alhamis, 17 ga Fabrairu, 2022, wata kotun daukaka kara ta bayyana bangaren Ganguje a matsayin wanda suke sahihan Shugabannin APC a Kano.

Da yake tsokaci kan rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar, Alwan ya ce “Saboda ba ya son tafiya, Buni ba ya son ficewa daga jam’iyyar, yana amfani da tsarin jam’iyyar wajen karbar kudi daga hannun mutanen da ke takara, abin da yake yi ke nan. .

“Lokacin da hukuncin kotun daukaka kara ya zo a ranar alhamis, kuma hakan ya shafi gwamnatin jihar Kano, kuma gwamnan Kano ya bukaci Mai Mala ya ba wa Abdullahi Abbas  takardar shaidar cin zabe, ka san abin da ya fada, sai ya nemi kudi. .

“Ya bukaci gwamna Ganduje ya ba shi kudi kafin ya ba da satifiket…. wannan ba yaudara bane?

“Mai girma gwamnan jihar Kano yana raye a yau, Mai Mala Buni yana raye, za ka iya tambaya a wurinsu, ya nemi kudi.”

Lokacin da Solacebase ta tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba a ranar Litinin kan zargin karbar cin hanci da Mai Mala Buni ya yi, ya musanta cewa ya san halin da ake ciki.

Kwamishinan ya dage cewa mai tuhumar Hassan Alwan ya bude maganar, idan yana da masaniyar yadda aka nemi cin hancin.

“Kana bukatar ka je ka tambayi Hassan Alwan ya gaya maka idan yana can lokacin da aka nemi cin hanci ko kuma ka je ka tambayi Mai Mala Buni kamar yadda Alwan ya zarge shi,” Muhammad ya mayar da martani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here