Rarara ya samu digirin girmamawa

WhatsApp Image 2025 09 20 at 17.28.15 750x430

Shahararren mawakin siyasa na Hausa, Dauda Kahutu Rarara, ya sami digirin girmamawa daga Jami’ar European American University, da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Commonwealth ta Jamhuriyar Dominica ta Panama.

An ba shi wannan girmamawa ne a lokacin bikin kammala karatun jami’ar karo na 23 da aka gudanar a Abuja, a ranar Asabar.

Rarara ya karɓi digirin a fannin kimiyya Ayyukan Jinƙai, Kiɗa da Nishaɗi.

Yayin miƙa takardar girmamawar a madadin shugaban jami’ar, Farfesa Idris Aliyu, wanda ke cikin majalisar gudanarwa ta jami’ar, ya bayyana cewa wannan lambar yabo na nuni da gudummawar Rarara wajen kiɗa da ci gaban ayyukan jin ƙai.

A nasa jawabin, wakilin jami’ar a Arewacin Najeriya, Dakta Musari Audu Isyaku, ya ce Rarara da wasu irinsu Alhaji Ahmed Saleh jnr., Farfesa Mustapha Abdullahi Bujawa da Farfesa Tarela Boroh, an karrama su ne saboda bajintarsu da tasirin da suke da shi wajen inganta rayuwar jama’a.

Rarara, cikin jin daɗinsa, ya ce wannan karramawa za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen faɗaɗa ayyukan jinƙai a jihar Katsina da sauran sassan Najeriya.

Ya kuma shawarci matasa da su rungumi haƙuri da jajircewa, yana mai cewa “hikima tana cikin yin aiki da manufa.”

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Umaru Dikko Radda, wanda ya halarci bikin, ya bayyana Rarara a matsayin “abin koyi kuma mai haɗa kan jama’a” wanda ya gudanar da ayyukan jinƙai da dama a faɗin Najeriya, tare da amfani da kiɗa wajen ƙarfafa haɗin kan al’umma.

Haka kuma, taron ya samu halartar manyan baki ciki har da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda; Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Ahmad Alkali; da kuma wasu ‘yan majalisar wakilai, ciki har da Abubakar Kabir Bichi, Nasiru Sani Danlami da Abdulmumini Zannah Bungudu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here