KUST ta musanta karbar alawus na Naira Biliyan 1 daga Gwamnatin Kano

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano

Kungiyar Malaman Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil ta musanta karbar alawus din ma’aikata na Naira Biliyan daya a hannun Gwamnatin Jihar Kano.

Wata sanarwa da kungiyar malaman jami’ar Aliko Dangote ta hadin gwiwa suka sanyawa hannu, tace babu wasu kudade da jami’ar ke amfani da su.

Karanta wannan: Katsina: An kashe Hakimi da ‘Dansa, tare da wasu mutane

Ta ci gaba da cewa, “Kungiyar ta lura da wasu kalamai a kafafen yada labarai da aka danganta ga kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata a ranar Litinin 8 ga watan Janairu, 2024 cewa gwamnatin jihar ta amince da raba sama da Naira biliyan 1 ga Yusuf.

Jami’ar Maitama Sule da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil domin biyan kudaden alawus na ilimi da ya wuce kima da sauran alkawurra.”

Karanta wannan: NITDA zata samar da cibiyar kere-kere ta zamani a Kano

Sanarwar ta cigaba da cewa, “bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, kungiyar na son jawo hankalin gwamnati da al’umma cewa kudaden da aka bayyana bai isa gare su ba.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa ‘yan kungiyar ASUU sun bukaci gwamnati ta binciki lamarin tare da daukar matakan da suka dace kan kudaden da aka bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here