Dan Sarauniya ya shawarci Ganduje ya koma makarantar allo

dan sarauniya
dan sarauniya

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Muazu Magaji, ya shawarci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya koma makarantar allo domin koyar yadda ake tafiyar al’umma, tare da sanin matsayin iyali a tsari na tafiyar da mulki.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da gwmnatin Kano ta fitar da sanarwa Gwamna Ganduje ya tafi kasar Amurka domin daukar kwas kan yadda ake gudanar da mulki a jami’ar Harvard.
Cikin wani rubutu da Muazu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya ce a wannan lokaci Gwamna Ganduje baya bukatar karin wani ilimi daga Jami’ar Havard dake kasar Amurka, domin kuwa karatun da yake dasu daga jam’ar Ahmadu Bello Zaria da jami’ar Ibadan sun ishe shi, illa yana bukatar ilimin da ya rasa tun a baya wato ilimin makarantar allo.

A cewa Dan Saurauniya ta haka ne Ganduje zai gane yadda ake tafiyar da dukiyar al’ummar da ake shugabanta da kuma da kuma amfanin nada mataimaka wanda zasu taimaka masa wajen gudanar da mulki na gari.

Ya kuma bukaci Gwamna Ganduje ya nemi tarihin Sayyadina Umar domin jin salon shuganacin sa, wanda idan yayi haka to baya bukatar zuwa jami’ar Harvard domin samun ilimin shugabanci.

A watan Afrilun shekarar 2020 ne Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kori Injiniya Muazu Magaji daga mukamin kwamishan ayyuka biyo bayan wasu kalamai da yayi wanda ke nuna cewa na murna da rasuwar tsohon shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Ganduje ya sake nada Dan Sarauniya a matsayin shugaban kwamitin aikin janyo bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, inda a nan ma Ganduje ya kore shi sakamakon rashin tabuka abun azo a gani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here