Ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC ta shirya zanga-zangar lumana a birnin Kano domin jaddada ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta, inda ta kuma miƙa wasiƙar buƙatu ga gwamnatin jihar Kano domin ɗaukar matakai na gaggawa.
Babban sakataren ma’aikata ga gwamnan Kano, Dakta Suleiman Wali, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na da kyakkyawar alaƙa da ƙungiyoyin ma’aikata, tare da bayyana zanga-zangar a matsayin shaida ta daidaito da fahimtar juna tsakanin gwamnati da ma’aikata.
Ya nuna cewa tsarin da aka bi wajen gudanar da zanga-zangar ya tabbatar da tattaunawa mai ma’ana maimakon rikici, yana mai jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin aiki tare da ƙungiyoyin kwadago ta hanyar tattaunawa.
Wali ya tabbatar wa ƙungiyar kwadago cewa batutuwan tsaro na samun kulawa sosai a jihar Kano, domin kuwa dukkan hukumomin tsaro na gudanar da ayyukansu yadda ya kamata domin ci gaba da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnan Kano zai duba wasiƙar da aka miƙa masa tare da tura abin da ke cikinta zuwa ga hukumomin da suka dace, ciki har da Shugaban ƙasa, domin ɗaukar matakan da suka dace.
Karin labari: Zanga-zanga a ƙasa baki ɗaya: Tinubu ya gana da shugabannin NLC
A baya, wakilin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa Muttaqa Yusha’u, ya bayyana cewa an shirya zanga-zangar ne bisa matsayar kwamitin zartarwa na ƙasa na ƙungiyar, domin wayar da kan jama’a kan matsalar rashin tsaro da kuma ƙarfafa zaman lafiya.
A cewarsa, rashin tsaro na shafar ma’aikata a fannoni daban-daban kuma ba za a samu ci gaba ba sai an samu tsaro da zaman lafiya.
Shi kuwa shugaban ƙungiyar kwadago a jihar Kano, Kabiru Inuwa, ya yaba da zaman lafiyar da ake samu amma ya buƙaci a ƙara ƙaimi domin hana yaduwar rashin tsaro.
NAN













































