Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da aka shigar a madadin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, da ‘yan uwansa biyu, inda suke neman kotu ta wanke su daga laifi a shari’ar da hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa ta gurfanar da su.
Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa hukumar NDLEA ta gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka isa a ci gaba da shari’ar, don haka ya wajaba a ba masu tuhuma damar kare kansu a gaban kotu.
Alkalin ya ce hujjojin da aka gabatar sun gamsar da kotu cewa akwai dalilan da suka isa a ci gaba da shari’ar, domin masu tuhuma su fitar da bayaninsu game da tuhumar da ake musu.
Hukumar NDLEA ta gurfanar da Abba Kyari da ‘yan uwansa, Mohammed Kyari da Ali Kyari, bisa zargin cewa sun kasa bayyana kadarorinsu gaba ɗaya, tare da ɓoye mallakar wasu kadarori da kuma karkatar da kuɗaɗe.
An tuhume su ne da karya dokar hukumar NDLEA da ta kasa da kuma dokar hana zamba da wanke kuɗi ta shekarar 2011, inda ake cewa laifukan suna ɗauke da hukunci mai tsanani.
Kotun ta ce, duba da dukkan hujjojin da aka gabatar, akwai dalilai masu tushe da suka isa a ci gaba da shari’ar, kuma ta umurci Abba Kyari da ‘yan uwansa su fara kare kansu daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Nuwamba mai zuwa.













































