Tsohuwar ministar jin ƙai ta yi martani kan zargin ta da ake da almundahanar naira biliyan 37

Hajiya Sadiya Umar Farouq
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Tsohuwar ministar jin ƙai da kare aukuwar bala’i ta Najeriya, ta mayar da martani kan wasu rahotannin da ke cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC, ta kama wani ɗan kwangila da aka yi zargin ya halasta kuɗin haram har naira biliyan 37, a binciken da take yi.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, Sadiya Umar Farouq, ta ce rahotannin ba komai ba ne, face wani yunƙurin ɓata mata suna.

A ranar Litinin ne jaridar Punch da wasu shafukan sada zumunta suka wallafa rahoton da cewa EFCC na ci gaba da bincike kan badaƙalar naira biliyan 37 da aka sauya wa ma’ajiya daga lalitar gwamnatin tarayya zuwa wasu asusu-asusu guda 38 masu alaƙa da ɗan kwangila James Okwete a bankunan kasuwanci.

Jaridar ta ƙara da cewa an bankaɗo zargin halasta kuɗin haram ɗin ne a ma’aikatar harkokin jin ƙai.

Sai dai tsohuwar ministar ta ce alaƙanta ɗan kwangilar da sunanta, ƙage ne kuma kwata-kwata ba ta san mutumin da ake magana kansa ba.

A cewarta, “James Okwete bai taɓa yi min aiki ba, kuma bai taɓa wakilta ta ba, ta kowacce irin siga”.

Sadiya Farouq ta ce tuni ta tuntuɓi lauyoyinta don su lalubo zaɓin da take da shi na neman kadi a kan abin da ta kira “zargin nufaƙa da aka yi mata”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here