Tinubu ya nemi majalisar Dattawa ta amince da sabon bashin cikin Gida na Naira Tiriliyan 1.15 don cike gibi a kasafin kuɗin 2025

tinubu 2

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya rubuta wasika zuwa majalisar Dattawa yana neman amincewa da sabon bashin cikin gida na naira tiriliyan 1.15 domin cike gibi da ke cikin kasafin kuɗin shekara ta 2025.

Wasikar ta shugaban ƙasa an karanta ta ne a ranar Talata yayin zaman majalisar dattawa da shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya jagoranta.

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa manufar ɗaukar bashin ita ce don cike gibi a ɓangaren kuɗi da kuma tabbatar da cikakken aiwatar da shirye-shiryen gwamnati da ayyukan da aka tsara a kasafin kuɗin shekarar.

Bayan karanta wasikar, shugaban majalisar dattawa ya miƙa buƙatar zuwa kwamitin majalisar kan bashin cikin gida da na waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wammako daga Sokoto ta Arewa, domin nazari.

An umurci kwamitin da ya kawo rahotonsa cikin mako guda domin ci gaba da matakan doka kan batun.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar na iya tattaunawa kan bukatar nan gaba kadan bayan rahoton kwamitin ya iso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here