Tinubu ya ƙaddamar da Asibitin ƙwararru da aka sanya wa sunansa a Kaduna

President Bola Tinubu Nyesom Wike and other government officials 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya ƙaddamar da asibitin kwararru mai gadaje 300 a dandalin Millennium da ke jihar Kaduna wanda aka sanya wa ginin sunan asibitin kwararru na Bola Ahmed Tinubu.

Asibitin ya ƙunshi sassa har guda tara da suka haɗa da na kula da lafiyar mata da yara sai na hoton sassan jiki da sashen kulawa ta musamman da sauran su.

Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta Najeriya ta kuma ce ta ba da izinin kafa cibiyar kula da cutar daji da kuma cibiyar nukiliya a rukunin.

Da yake jawabi a wurin bikin, gwamnan jihar Uba Sani, ya buƙaci Tinubu ya sanya baki wajen gina cibiyar kula da cutar daji.

Da yake mayar da martani, Tinubu ya yaba wa gwamna Uba Sani bisa ayyukan raya kasa da kuma tasirinsa ga al’ummar jihar.

Tinubu ya isa Kaduna ne a ranar Alhamis domin kaddamar da ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta gudanar.

Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ne ya tarbe shi tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, da Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli.

Sauran gwamnonin da suka tarbi shugaban sun hada da Hope Uzodimma na jihar Imo da Babajide Sanwo-Olu, na Lagos da Biodun Oyebanji na Ekiti da Monday Okpebolo na Edo da Umar Namadi na Jigawa sai kuma AbdulRahman Abdulrazaq gwamnan jihar Kwara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here