Sufeton ƴan sandan Najeriya ya haramtawa ‘yan sanda daukar bindiga cikin fararen kaya

IGP kayode egbetokun

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, ya ba da umarnin cewa daga yanzu, “Ba za a sake ganun wani dan sanda dauke da makamai sanye da fararen kaya (mufti) ba.”

Ya kuma yi kakkausar gargadi ga dukkan jami’ai dangane da tauye hakkin bil’adama, inda ya jaddada aikin rundunar na kiyaye wadannan hakkoki.

Da yake magana a yayin wani taron sirri da ya kira da shugabannin ‘yan sanda, a jiya, Egbetokun ya fusata da irin wannan aika-aikar, bayan da ya samu korafe-korafe daban-daban dangane da take hakkin bil’adama ta hanyoyin korafe-korafe na rundunar.

Karin labari: IGP ya ba da umarnin aiwatar da sabuwar inshora daga ranar 1 ga Fabrairu

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Mista Muyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Litinin, ta ce taron na da nufin kara tabbatar da ingancin aiki da kuma tabbatar da gudanar da ingantaccen aiki a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya.

“IGP din ya bayyana cewa ba za a amince da duk wani hali da ya keta hakkin dan Adam ba kuma duk wanda ya aikata zai fuskanci mummunan sakamako.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here