Shugaban kasar Ukraine ya yi hatsarin mota

25e3ef8b fe59 47fa 8fcd 5ea3205623cf
25e3ef8b fe59 47fa 8fcd 5ea3205623cf

Hatsarin mota ya rutsa da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a Kyiv babban birnin kasar.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar ya ce wata motar fasinja ce ta daki tawagar motocin da shugaban ke ciki ranar Laraba a birnin na Kyiv.

Shugaban dai bai samu munanan raunuka ba kamar yadda likitansa ya bayyana.

Tuni dai aka yi wa diraban motar fasinjan magani, yayin da kuma daga bisani aka dauke shi a motar daukar masara lafiya

Hadarin ya faru ne bayan da Mista Zelensky ya ziyarci birnin Izyum da ke arewa maso gabashin kasar, wanda dakarunsa suka kwace daga hannun sojojin Russia.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here