Gwamnatin tarayya ta sanar da samun nasarar rage farashin allurar kariya daga kwayar cutar HIV mai suna lenacapavir, daga dala 28,000 zuwa dala 40 kacal ga mutum ɗaya.
Misis Toyin Aderibigbe, Mataimakiyar Darakta a sashen hulɗa da Jama’a da tsare-tsare ta hukumar kula da Cutar Kanjamau ta Ƙasa (NACA), ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
Daraktan Janar ma NACA, Dakta Temitope Ilori, wanda ya halarci taron ne tare da shugabannin duniya a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA), ya nuna kwarin gwiwa cewa rangwamen zai bai wa miliyoyin mutane a Najeriya da sauran ƙasashe damar samun wannan magani.
Karanta: UNGA80: Shettima ya gana da Guterres,tare da tattauna batun neman kujera a kwamitin tsarona MDD
Rahotanni sun nuna cewa lenacapavir na da tasiri har kashi 100 bisa 100 wajen hana sabbin mutane kamuwa da cutar HIV.
Ilori ya ce wannan yarjejeniya ta tarihi tana kawo sabon fata da sauƙi ga masu fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.
Wannan ci gaba ya biyo bayan haɗin gwiwa da ƙungiyoyi irin su UNITAID, Cibiyar Tallafin Kiwon Lafiya ta Clinton (CHAI), Wits RHI, Dr. Reddy’s Laboratories Ltd. (DRL) da Gidauniyar Gates.
Gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa burinta shi ne ƙara faɗaɗa hanyoyin kariya, ƙarfafa tsarin kiwon lafiya, da hanzarta kawo ƙarshen cutar HIV a matsayin barazana ga lafiyar jama’a nan da shekarar 2030.
NAN













































