Mutane 33 sun mutu, wasu 33 sun jikkata a haɗɗuran lantarki da dangogin su a cikin watanni uku — NERC

NERC 5

Sabbin bayanai daga Hukumar kula da lantarki ta ƙasa sun nuna cewa mutane 33 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 33 suka jikkata sakamakon haɗɗuran da suka shafi lantarki a faɗin ƙasar nan cikin watanni uku.

Rahoton zangon kashi na uku na shekarar 2025 ya nuna cewa an samu jimillar haɗɗuran lantarki 57 a duk ƙasar, inda aka rarraba su a yankunan rarraba wutar lantarki daban-daban.

Rahoton ya bayyana cewa yankunan rarraba lantarki na Ikeja da Kano ne suka fi samun haɗɗura a wannan zangon, inda kowanne yanki ya samu hatsurra 10.

A yankin Ikeja, an samu mutane huɗu da suka mutu da kuma shida da suka jikkata, yayin da a yankin Kano aka samu mutane shida da suka mutu da huɗu da suka jikkata.

Sauran yankunan da suka samu irin waɗannan haɗɗura sun haɗa da Abuja, Jos, Aba, Port Harcourt, Enugu da Yola, yayin da yankunan Eko da Kaduna da kuma Kamfanin watsa lantarki na Najeriya.

A mafi yawan lokuta, haɗɗuran sun haifar da mummunan rauni ko mutuwa, ko duka biyun.

Rahoton ya nuna cewa ayyukan rashin tsaro da yanayi masu haɗari su ne suka fi haddasa raunuka, kuma sun yi daidai da yawan mutuwar da aka samu.

Katsewar wayoyin lantarki ta kasance ɗaya daga cikin manyan haɗurra, inda ta haddasa mutuwar mutane 10 da jikkatar wasu bakwai.

Haka kuma, ayyuka rashin tsaro sun haddasa mutuwar mutane 10 da jikkatar 18, abin da ke nuna kura-kurai na ɗan Adam da raunin tsarin tsaro.

Har ila yau, shiga ko amfani da na’urorin lantarki ba bisa ka’ida ba ya taimaka wajen ƙaruwa adadin waɗanda suka jikkata, inda hakan ya jawo mutuwar mutane biyu da jikkatar uku.

Lalata kayan aiki ta hanyar barna ma ta haddasa mutuwar mutane biyu a wannan zangon.

Hukumar ta bayyana cewa ta fara bincike kan dukkan haɗɗuran da aka samu, tare da ɗaukar matakan da suka dace.

Rahoton ya ƙara da cewa an rage yawan haɗɗuran da mace-mace idan aka kwatanta da zangon da ya gabata, sai dai adadin waɗanda suka jikkata ya ƙaru, abin da ke nuna cewa har yanzu akwai buƙatar ƙarfafa tsaro a bangaren rarraba lantarki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here