Hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa Kwastam ta bayyana cewa daga Litinin, za a daina karɓar haraji kan kaya da ƙimarsu ba ta haura dalar Amurka 300 ba.
Wannan sabuwar doka ta samu amincewar kwamitin hukumar a zaman da suka gudanar karo na 63, karkashin jagorancin Ministan Kuɗi, Wale Edun.
Mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Maiwada, ya ce wannan tsari wanda ake kira “De Minimis” na da nufin inganta cinikayyar kasuwancin Internet wato e-commerce ta ƙasashen waje, rage jinkiri wajen shige da fice da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
Ya ce tsarin ya yi daidai da abin da ake amfani da shi a ƙasashen duniya wajen bayar da kariya ga kananan kayayyaki.
Karanta: Babu gudu ba ja da baya kan batun yajin aiki – NUPENG ta nanata
Kwastam ta ce wannan sassauci zai shafi kaya da aka shigo da su ƙarƙashin e-commerce, kayan matafiya, da kuma ƙanana lodin kaya, muddin ba haramun ba ne ko kuma an takaita shigarsu.
Amma an kayyade hakan ba zai wuce shigo da kaya sau huɗu a shekara ba.
Hukumar ta yi gargadi cewa duk wanda ya ƙi bin wannan tsari zai fuskanci hukunci kamar ƙwace kaya, kamawa da sauran hukunci da aka tanada a dokar Kwastam ta 2023.
An kuma kafa tashoshin taimako domin sauƙaƙa fahimtar wannan sabuwar doka ga masu ruwa da tsaki.
Bugu da ƙari, hukumar ta tattauna kan wasu batutuwan ladabtarwa inda ta rage matsayin wasu jami’ai biyu saboda aikata rashin da’a, sannan kuma ta dawo da wasu biyu bayan sake nazari.
Ta kuma ja kunnen jami’anta kan amfani da miyagun ƙwayoyi da sauran halaye marasa kyau, tana mai jaddada cewa ba za ta lamunta da hakan ba.
Kwastam ta ce za ta ci gaba da yin aiki da gaskiya da ladabi wajen sauke nauyin da aka dora mata tare da tabbatar da sahihin tsarin aiki domin ƙarfafa amincewar jama’a.












































