Kwankwaso ya lissafo sharaɗi kafin komawa APC

Rabiu Kwankwaso (1)

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gindaya sabon sharaɗi kafin yanke shawarar komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Kwankwaso ya bayyana matsayarsa ne a wani bidiyo da hadiminsa Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook, inda ya nuna cewa ba zai shiga APC ba sai an cimma yarjejeniya mai ƙarfi tare da fayyace rawar da zai taka da tsare-tsaren da za su shafi talakawa, musamman dimbin magoya bayansa.

Ya nuna rashin amincewa da shiga jam’iyyar ba tare da cimma cikakkiyar fahimta ba, muhimmancin sanin makomar gwamnatin Jihar Kano da tsarin siyasar da suke da shi kafin duk wata sauya sheƙa.

Kwankwaso ya tunatar da abubuwan da suka faru a baya inda bangarensa ya taimaka wajen kafa gwamnati amma daga bisani aka ware su daga harkokin mulki, lamarin da ya sa suka bar jam’iyyar a wancan lokaci.

Karanta: Kwankwaso ya zargi gwamnatin Kano da matsa lamba kan zaɓaɓɓun shugabanni da waɗanda aka naɗa kan su shiga APC

Ya bayyana cewa har yanzu babu tabbacin da aka bayar cewa za a bar su su riƙe gwamnatin da suke da ita ko su ci gaba da tafiyar da tsarin siyasar su bayan shiga APC, abin da ke sa ya nemi a fayyace masa matsayinsa a sarari.

Kwankwaso ya kuma nuna mamaki kan kalaman da tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi kan batun, yana mai cewa lamarin bai shafe shi ba, tare da jan hankalinsa da ya mayar da hankali kan harkokinsa a jam’iyyar PDP.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa taron da aka yi kan batun ya samu halartar mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, kwamishinan kimiyya da fasaha Yusuf Kofar Mata, shugaban NNPP na jihar da aka dakatar Hashim Sulaiman Dungurawa, da sauran manyan magoya bayan Kwankwaso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here