Kwamishinan Fasaha Yusuf Kofar Mata ya yi murabus

images (3) (23)

Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire a Jihar Kano, Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya sanar da saukarsa daga muƙaminsa.

A cewarsa ta cikin wata sanarwa da ya fitar da tsakar ranar yau Lahadi, ɗaukar matakin ya biyo bayan kaucebwa daga tsarin gwagwarmayar siyasar da aka yi wadda da ita aka kafa gwamnati.

Yusuf Kofar Mata ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce ya yanke shawarar sauka daga muƙamin domin bin ƙa’ida da akidar siyasar da aka gina gwamnatin jihar Kano mai ci i a kai.

Ya nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki, sannan ya miƙa godiya ta musamman ga Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa damar da suka ba shi.

Haka kuma, Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya gode wa al’ummar Jihar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi a lokacin da yake gudanar da ayyukansa a ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da ma’aikatar kimiyya, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma sauran muhimman ayyukan da ya ce ya aiwatar domin ci gaban jihar.

Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, dai shi ne kwamishina na farko da ya ajiye mukaminsa tun lokacin da aka fara dambarwar Siyasa tsakanin gwamnan Kano da Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here