Wata kotun majistare da ke Kuje, Abuja, ta bayar da belin mai fafutukar kare hakkin dan adam kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, tare da ɗan’uwan jagoran ƙungiyar IPOB Nnamdi Kanu, Prince Emmanuel Kanu, lauya Aloy Ejimakor da wasu mutum goma sha ɗaya.
Kotun ta bayar da belin ne kowane ɗaya cikin su a kan kuɗi naira dubu ɗari biyar, tare da masu bayar da belin guda biyu da ke da irin wannan daraja ta kuɗi.
Idan za a iya tunawa an kama su ne saboda zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 20 ga Oktoba, inda ake zargin sun tayar da tarzoma da haddasa tashin hankali.
An ruwaito cewa, Sowore an kama shi ne daga baya ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan ya halarci zaman shari’ar Kanu don nuna goyon baya gare shi.
Lauyoyin masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa waɗanda ake zargin za su ci gaba da fuskantar shari’a saboda tada hankali da tayar da fitina a bainar jama’a.
Sai dai kotun ta amince da buƙatar lauyoyinsu na bayar da beli bayan ta saurari korafi da dalilan da aka gabatar a zaman ranar Juma’a.
Kotun ta umarci a sake su bayan cika sharuɗɗan beli yayin da ake jiran ci gaban shari’ar.
Cikakken labarin na nan tafe……












































