Gwamnan jihar Yobe Mai mala Buni ya nada masu bashi shawara guda 24.
Hakan na dauke cikin wata sanarwa da mai yada labaran sakatarengwamnatin jihar, Shuaibu Abdullahi, ya fitar ranar Litinin.
Wadan da aka nada a matsayin mashawartan su ne: Dakta Kole Shettima, Dakta Mahmoud Bukar Maina, Gen.Dahuru Abdulsalam, Usman Adamu Kabarma, Alhaji Mohammed Lamin, Alh. Mala Musti, Alh. Bukar Dauda, , Hon. Abdullahi Usman Kukuwa , Sen. Alkali Abdulkadir Jajere, Hon. Yerima Lawan Yunusari, Hon. Mohammed Samaila Nguru , Alh. Mohammed Kadai da kuma Hon. Zanna Ali Machina.













































