Gwamnatin Kano ta saka dokar takaita zirga-zirga saboda zaben kananan hukumomi

Abba Kabir Yusuf 595x430

Jihar Kano, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro, ta sanya dokar hana zirga-zirga a fadin jihar daga ƙarfe 12 na dare zuwa ƙarfe 6 na yamma a ranar Asabar.

Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Baba Halilu Dantiye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Dantiye ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro don gudanar da sahihin zaben kananan hukumomi da aka shirya yi a ranar 26 ga Oktoba.

Dantiye ya yi kira ga mazauna jihar su bi dokar hana zirga-zirga, yana mai jaddada kudirin gwamnatin wajen tabbatar da sahihi kuma ingantaccen tsarin zabe.

Wannan doka ta shafi mutane da motoci a dukkanin kananan hukumomi 44 da mazabu 484 na jihar.

Wannan matakin an dauke shi domin tabbatar da doka da oda tare da kare duk wata barazanar da ka iya kawo cikas a lokacin zabe. Sai dai an ware mutanen da ke da alhakin aikin zabe na hukuma da kuma masu ayyukan da suka zama wajibi.

Gwamnatin Jihar Kano na kira ga dukkan jama’a su bada goyon baya wajen ganin an samu nasarar wannan yunkuri, tare da la’akari da cewa bin dokar yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da nasarar zaben.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here