Fashin gidan yarin Kuje: gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen ‘yan ta’adda 69 da suka tsere

Nigerian correctional service reveals the identities of the fleeing Imo inmates 1
Nigerian correctional service reveals the identities of the fleeing Imo inmates 1

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta bayyana neman wasu kasurguman mutane 69 ruwa a jallo da suka tsere daga fashin magarkamar Kuje ta babban birnin tarayya Abuja.

Dangane da bayanin da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Umar ya fitar, wadanda suka tsere an ce ‘yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ne.

Amma ba’a ga suna ko hoto na Hamisu Wadume, wanda babban mai garkuwa da mutanene a jihar Taraba, da kuma hoton kumandan ‘yan Boko Haram Al Barnawi ba, kuma hukumar kula da gidajen yarin Najeriya bata ce komai akai ba.

Hukumar ta fitar da suanaye dauke da hotona na wadan da suka tsere daga gidan yarin Kuje.

daga cikin sunayen akwai Abdulkareem Musa, Abdulsalami Adamu, Abubakar A Habibu, Abubakar M Sadiq, Abubakar Mohammed, Akibu Musa Danjuma, Amodu Omale Salihu, Ismaila Idris Abdullahi.

Sauran sun hada da Suleiman Zacharia, Sunday Micheal, Baluye Modu, Adamu Hagola, Ibrahim Musa, Auwal Abubakar, Muktar Umar and Musa Umar, amongst others.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here