Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar NNPP, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya isa turai domin gabatar da tuntuba tare neman goyan baya.
kamar yadda mai taimakamasa kan kafafen sadarwa ya wallafa a shafin sa na tuwita. Sanata Kwankwaso ya fara ziyarar ne da kasar Faransa inda ya yi wata ganawa ta musamman da Thomas Gassiloud, wani mai fada aji a Faransa.
Ya kuma ziyarci Kwamitin tsaro na Majalisar Dokokin Faransa a birnin Paris, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi moriyar juna tsakanin shugabannin biyu.













































