Babban tushe daga cikin rundunar sojin Najeriya ya bayyana sunayen da kuma sassan aiki na manyan jami’an soji 16 da ake tsare da su a hukumar leƙen asirin tsaron ƙasa bisa zargin shirin kifar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Rahotanni sun gano cewa daga cikin jami’an, 12 suna cikin rundunar Infantry Corps, wadda ke da alhakin yaƙin ƙasa kai tsaye.
Ɗaya yana cikin rundunar sadarwa ta Signals Corps, yayin da wani ke cikin rundunar Ordnance Corps da ke kula da kayan yaƙi, motoci da makamai.
Daga cikin jami’an akwai Brigediya Janar Musa Abubakar Sadiq wanda ake zargin shi ne jagoran shirin juyin mulkin.
Rahotanni sun nuna cewa a watan Oktoba na shekarar 2024 an taɓa tsare shi bisa zargin karkatar da kayan tallafin shinkafa da kuma sayar da kayan aikin soja ga masu sayen shara.
Sauran jami’an sun haɗa da Kanal M.A. Ma’aji daga Jihar Neja, Laftanar Kanal S. Bappah daga Bauchi, Laftanar Kanal A.A. Hayatu daga Kaduna, da Laftanar Kanal P. Dangnap daga Filato wanda aka taɓa gurfanar da shi a gaban kotun soji a shekarar 2015 saboda laifukan da suka shafi yaƙin Boko Haram.
Haka kuma akwai Laftanar Kanal M. Almakura daga Nasarawa, Meja A.J. Ibrahim daga Gombe, Meja M.M. Jiddah daga Katsina, Meja M.A. Usman daga Abuja, Meja D. Yusuf daga Gombe, Meja I. Dauda daga Jigawa, Kyaftin Ibrahim Bello, Kyaftin A.A. Yusuf, da Laftanar S.S. Felix.
Sai kuma jami’ai biyu daga sauran rundunoni: Laftanar Kwamanda D.B. Abdullahi daga Rundunar Ruwa, da Squadron Leader S.B. Adamu daga Rundunar Sojin Sama, waɗanda ake ci gaba da bincike kan rawar da suka taka a zargin juyin mulkin.
An kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kai samame a gidan tsohon karamin ministan albarkatun mai Timipre Sylva da ke Maitama, Abuja, bayan samun bayanan sirri da ke zargin sa da shiga cikin tattaunawa da wasu daga cikin jami’an da ake tsare da su.
Sylva ya tabbatar da samamen amma ya musanta samun hannu a lamarin.













































