Buhari ya nada Sarkin Kano a matsayin uban wata jami’a

EDACE5D9 E028 438C 884E BD8C21C9FB9D
EDACE5D9 E028 438C 884E BD8C21C9FB9D

Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin uban jami’ar Calabar ta jihar Cross River.

Solacebase ta ruwaito cewa, Shugaban Jami’ar, Janar Matthew Luther Agwai (RTD) ne ya bayyana hakan, a ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da ya jagoranci mambobin majalisar a ziyarar taya murna da suka kai wa Sarkin a fadarsa.

Agwai ya ce al’ummar Jami’ar Calabar ta cika da murna da nadin da aka yi wa Sarki Aminu Ado Bayero a matsayin sabon uban  Jami’ar.

Janar Matthew Luther Agwai (RTD) ya ci gaba da cewa da dimbin gogewar sarkin, jami’ar za ta samu babban matsayi na ƙwararrun ilimi.

Da yake mayar da martani, Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna jin dadinsa ga Gwamnatin Tarayya da ta same shi da ya cancanci zama Shugaban Jami’ar.

Muna tattaunawa da jami’ar Calabar da ke jihar Cross River, kuma za mu yi iya kokarinmu wajen ganin an samu Nagartaccen Ilimi.

Sarkin ya nemi goyon bayan daukacin ‘yan Majalisar da na Jami’ar wajen ganin an cimma burin da ake so.

Daga nan sai ya yaba da namijin kokarin da Shugaban Jami’ar, Janar Matthew Luther Agwai, da ‘yan uwa na Jami’ar suka yi, inda ya bukace su da su ci gaba da gudanar da aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here