Bankin Ja’iz ya samu lambar girmamawa ta babban bankin Musulunci na shekarar 2024

GIFA AWARDS 750x430

Bankin Jaiz, bankin da baya ta’ammali da kudin ruwa na farko a Najeriya, ya samu lambar girmamawa a matsayin babban bankin Musulunci na shelarar 2024.

A yayin taron koli na harkokin kudi na Islama na duniya da bikin bayar da kyaututtuka da aka gudanar a Jamhuriyar Maldives, bankin Jaiz ya zarce wasu bankuna biyu da aka zaba a fanni daya da suka lashe kyautar babbar lambar yabo.

Farfesa Humayon Dar, shugaban kungiyar GIFA, ya bayyana cewa an zabi bankin Jaiz ne bayan cikakken kimantawa bisa ka’idoji da yawa da kwamitin bayar da kyaututtuka na GIFA ya zayyana.

An amince da bankin ne don haɓakar sa na musamman, ƙirƙira, da ayyukan kuɗi, waɗanda suka taimaka, lamarin da ya ƙarfafa jagorancinsa a cikin masana’antar.

Haruna Musa, Manajan Darakta/Shugaba na Bankin Jaiz, ya bayyana jin dadinsa da karbar kyautar.

Ya jaddada cewa amincewar ya yi daidai da dabarun bankin na zama daya daga cikin manyan cibiyoyin hada-hadar kudi na Afirka wadanda ba su da ruwa a cikin shekaru biyar.

Ya kuma kara da cewa bankin Jaiz ya taba lashe kyautar bankin Musulunci mafi inganci na GIFA a shekarar 2020 da 2021.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here