Ganawar dai na zuwa ne a daidai Lokacin da babban zaben shekara ta 2023 ke kara gabatowa a Nigeriar, ko da yake dai tsofaffin shugabannin, Janar Babangida da Janar Abdussalam ba su ce wa manema labarai komai ba akan wannan ganawar.
Amma Dakta Jonathan ya ce ya zo Minna ne domin gaisuwa ga wadannan tsoffin shugabanni, amma dai ya yi amfani da wannan dama wajan yin kira ga ‘yan Nigeria da su zabi shugaban da zai kawo cigaba a kasa baki daya.
Ya kuma kara da cewa “dukkaninmu muna yiwa kasarmu fatan alheri ga matasanmu, kuma zabe mai zuwa ya zama wajibi mu zabi wanda zai mana shugabanci na gari, mutumin da Najeriya ce a gabansa ba wai biyan bukatunsa ba.”
VOA











































