Barau ya yiwa Shekarau da Gwarzo maraba da shiga APC

imgonline com ua twotoone KIU3DX0dvIoO

Matamakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo barka da shigowa jam’iyyarsu ta APC.

Cikin ‘yan kwanakin nan ne dai manyan ‘yan siyasar suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP a Kano, inda suka bayyana rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi a matsayin dalilinsu na barinta.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Sanata Barau kan hulda da jama’a da yada labarai, Malam Isma’il Mudashir, ya fitar, Barau ya bayyana sauya shekar jiga-jigan a matsayin wani abu da zai karawa jam’iyyar karfi yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.

“Ina yi wa tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da tsohon bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo barka da shigowa jam’iyya mafi girma a fadin Africa, APC.” Inji Barau.

Sanatan Barau, wanda shi ne mutum na farko da ya zama matamakin kakakin majalisar kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirika ta Yamma (ECOWAS), ya jaddada cewa shigar mutanan ya sake tabbatar da samun nasarar jam’iyyar a zabukan shugaban kasa da gwamna da kuma ‘yan majalisu.

Haka zalika, Barau ya kara da cewa sauya shekar da ‘yan adawa suke yi a jihar ya wannan irin yarda da kamun ludayin shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here