Babban alkalin kotu ya sake tura shari’o’in badaƙalar kuɗi da kwace kadarori da ake yi wa Malami zuwa wani alkalin

images 12

Babban alkalin Kotun Tarayya, Mai shari’a John Tsoho, ya sake tura shari’ar badaƙalar kuɗi da kuma ƙarar kwace kadarori guda 57 da aka shigar kan Abubakar Malami zuwa hannun Mai shari’a Obiora Egwuatu na Kotun Tarayya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa an riga an sanya ranakun sauraron shari’o’in biyu, waɗanda yanzu Mai shari’a Egwuatu ne zai saurara.

An tsara sauraron ƙarar kwace kadarorin mai lamba FHC/ABJ/CS/20/2026 a ranar 12 ga Fabrairu, yayin da shari’ar laifin wankiyar kuɗi da ake tuhumar Malami, tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya, matarsa Hajia Asabe Bashir da ɗansa Abdulaziz, aka sanya ta a ranar 16 ga Fabrairu.

Tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya, matarsa da ɗansa ana sa ran za a sake gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda 16 na laifin wanke kuɗi mai lamba FHC/ABJ/CR/700/2025 a gaban sabon alkalin shari’a, sakamakon sake tura shari’ar.

Bisa tsarin shari’a, duk shari’ar da aka sake tura wa wani alkalin ana fara ta ne daga farko ba tare da jingina da hukunci ko fahimtar da kotun da ta gabata ta yi ba, sai dai idan ɓangarorin sun amince.

NAN ya rawaito cewa a ranar 30 ga Disamba 2025, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta gurfanar da Malami, Asabe da Abdulaziz a gaban Mai shari’a Emeka Nwite, wanda ya zama alkalin hutu a lokacin hutun Kirsimeti.

An tuhume su da laifukan wankiyar kuɗi da darajarsu ta kai N8,713,923,759.49, kuma dukkansu sun musanta laifukan.

An tsare Malami da ɗansa a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da aka tsare Asabe a gidan gyaran hali na Suleja, kafin daga bisani kotu ta ba su beli na Naira Miliyan 500 kowannensu tare da masu tsaya musu biyu-biyu a ranar 7 ga Janairu.

A ranar 6 ga Janairu kuma, Mai shari’a Nwite ya bayar da umarnin kwace kadarori guda 57 da ake zargin kudaden haramtattun ayyuka ne da ke da alaƙa da Malami, domin mika su ga gwamnatin tarayya na wucin gadi.

Alkalin ya bayar da umarnin ne bayan karɓar buƙatar gaggawa daga lauyan EFCC, Ekele Iheanacho SAN, inda ya umarci hukumar ta wallafa sanarwar a jaridar ƙasa domin masu ruwa da tsaki su bayyana dalilin da ya sa kada a kwace kadarorin gaba ɗaya cikin kwanaki 14.

Kadarorin, waɗanda darajarsu ta kai Biliyoyin Naira, suna cikin Jihohin Abuja, Kebbi, Kano da Kaduna.

Sai dai Malami ya ƙalubalanci ƙarar kwace kadarorin, inda ya roƙi kotu ta yi watsi da ita, yana mai cewa EFCC ta samu umarnin ta hanyar ɓoye muhimman bayanai da kuma ba da bayanan da ba su dace ba.

Ya kuma bayyana cewa shari’ar tauye masa haƙƙin mallakar dukiya, haƙƙin rashin zargi kafin hukunci da kuma haƙƙinsa na rayuwa cikin kwanciyar hankali tare da iyalansa.

NAN ya ƙara da cewa Malami da ɗansa Abdulaziz suna kuma fuskantar wata shari’a daban a gaban Hukumar DSS kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin ta’addanci a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here