David Umahi da mataimakinsa, Kelechi Igwe sun samu umarnin wucin gadi daga babbar kotun jihar Ebonyi, inda ta umarce su da kada su bar ofisoshinsu.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri gaggawa da lauyan mutane biyun , Roy Umahi ya gabatar dangane da hukuncin 3(3) na dokokin babbar kotun jihar Ebonyi.
Kotun dai a ranar 28 ga watan Fabrairun 2022 ta yanke hukuncin cewa Gwamna Umahi da mataimakinsa ba su karya wata doka ba ta hanyar sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC ba.
Kotun karkashin mai shari’a Henry Njoku ta yi watsi da karar ne saboda rashin cancantar ta kuma ta ci tarar wanda ya shigar da karar, Sunny Ogbuoji, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar APC kuma ya tsaya takara a zaben gwamna na 2019.
Sai dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar 8 ga watan Maris ta yanke hukunci kan irin wannan batu, inda umarci gwamnan da mataimakinsa da su bar kujerunsu.
A halin da ake ciki kuma, Kotun ta kori Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru da wasu ‘yan majalisa 14 saboda sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP a ranar Alhamis, sun ce ba su gamsu da hukuncin ba.
A ranar Talata ne mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ayyana kujerun kakakin majalisar Nwifuru da wasu ‘yan majalisa 14.
Alkalin kotun ya umarci INEC da ta gudanar da zaben cike gurbi na cike gurbi, a mazabun cikin kwanaki 90.












































