Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, ya bayyana cewa ya zama dole gwamnati ta daina nada ’yan siyasar da suka gaza da kuma mutanen da ba su da cancantar ilimi a matsayin shugabannin jami’o’in Najeriya domin hakan yana lalata ingancin harkokin ilimi a kasa.
Ya yiwannan kira ne yayin gabatar da lacca karo na uku ta tunawa da Abdullahi Mahadi da aka gudanar a Jami’ar Gombe, inda ya jaddada cewa jami’a na bukatar shugabanni masu hangen nesa da gogewar gudanarwa ba masu biyayya ta siyasa ba.
Ya ce dole a tabbatar da cewa shugabannin jami’o’i sun fito ne daga cikin wadanda suka kware wajen gudanar da harkokin ilimi, domin tsarin nada shugabanni bisa la’akari da siyasa yana haifar da koma baya da kuma tabarbarewar ingancin gudanarwa a manyan makarantu.
Farfesa Jega ya yi nuni da cewa tsoma bakin siyasa wajen nada shugabannin jami’a, shugabannin majalisun jami’a, da sauran manyan mukamai na kara dagula lamuran gudanarwa tare da haifar da matsaloli da ke tauye ingancin ilimi a matakin kasa.
Ya yi gargadin cewa sai an yi watsi da tsoma bakin siyasa, a rungumi tsarin nada shugabanni bisa cancanta da gaskiya, sannan a tabbatar da bude kofa ga kowa domin samun ingantaccen zabi, idan ba haka ba Najeriya za ta ci gaba da samar da daliban da ba su da isasshen shiri ga ci gaban kasa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa taron laccar ya tara masana, ’yan siyasa, dalibai da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, wadanda suka jaddada bukatar gaggawar gyara domin dawo da mutunci da nagartar tafiyar da jami’o’in Najeriya.










































