Ƙungiyoyin da ke rashin ci gaban al’umma (CSOs) da ke aiki kan yaki da cin hanci, gaskiya da ɗaukar nauyin al’umma sun nemi a gaggauta gudanar da bincike kan Ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, bisa zargin ɓoye kadarori, tara haramtattun dukiya da kuma karya dokokin bayyana kadarori na Najeriya.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ƙungiyoyin sun bukaci hukumomin yaki da cin hanci irin su (EFCC), (ICPC), (CCB), majalisar ƙoli kan harkokin shari’a ta Ƙasa (NJC), da hukumar tara haraji ta Ƙasa (FIRS), da su fara bincike ba tare da la’akari da matsayin siyasa ko mukami ba.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa sanarwar da ƙungiyoyi 52 suka rattaba hannu a kai ta yi nuni da cewa babu wani jami’in gwamnati da ya wuce doka.
Ƙungiyoyin sun jaddada muhimmancin hukumar CCB wajen tabbatar da gaskiya a aikin gwamnati, tare da bukatar ta kauce wa duk wata katsalandan ta siyasa.
Sun ce dole ne a rika duba bayanan kadarorin manyan jami’ai a lokacin mulki, ba kawai a lokacin shiga ko barin aiki ba.
Karanta: Zargin Zamba: Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon Ministan Wutar Lantarki
Sanarwar ta kuma nuna rahotanni masu karfi da ke alaƙanta Wike da matarsa, Mai Shari’a Eberechi Suzzette Nyesom-Wike ta Kotun ɗaukaka ƙara, da kadarori da ba a bayyana ba.
Rahotanni sun ce, sun mallaki gidaje uku masu tsada a kusa da tafki a Florida, Amurka, tsakanin 2021 zuwa 2023, sannan suka mika su ga ‘ya’yansu.
Haka kuma, akwai zargin amfani da kamfanonin takarda (shell companies), motocin alfarma, da kadarori a Abuja da aka ware wa ‘yan uwa.
Ƙungiyoyin sun kuma tunatar da tsohon zargi na karkatar da dala miliyan 300 da aka ware don gyaran muhalli a Ogoniland zuwa harkokin kasuwanci na sirri, ciki har da cibiyar sayar da kaya a Fatakwal.
Bugu da ƙari, Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar FCT ta zargi ministan da rabon filaye ba bisa ka’ida ba a Abuja, inda rahotanni suka nuna cewa wasu filaye na musamman sun shiga hannun ‘yan uwansa.
Sanarwar ta ce, “Idan aka tabbatar da waɗannan zarge-zargen, ba wai kawai karya dokokin yaki da cin hanci bane, har ila yau babban cin amana ne ga jama’a.”
Kungiyoyin sun bukaci cikakken bincike kan kadarorin Wike a matsayin gwamna da minista, a yi binciken kudi na musamman kan mu’amalolin shi da iyalinsa, tare da wallafa sakamakon bincike a fili.
Sun kuma yi gargadin cewa idan hukumomin yaki da cin hanci suka kasa daukar mataki mai karfi, hakan zai ƙara ƙarfafa cin hanci, amma idan aka yi bincike cikin gaskiya, zai dawo da martabar hukumomin Najeriya a idon jama’a.
Sun kuma roki ƙungiyoyin duniya da masu bayar da tallafi su sa ido sosai kan lamarin, domin tabbatar da cewa Najeriya ta nuna gaskiya da adalci.
Sun kuma jaddada cewa wannan shari’ar za ta kasance gwaji ga hukumomin yaki da cin hanci na ƙasa.
A ƙarshe, ƙungiyoyin sun shawarci gwamnati ta yi amfani da wannan al’amari wajen kafa tsarin hadin kai da wayar da kan jama’a don yaki da cin hanci, musamman tsakanin manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a siyasa. Sun ce, “Doka dole ta kasance bai daya ce ga kowa, ba tare da la’akari da mukami ko tasirin siyasa ba.”













































