CBN ya musanta ɗaga ranar ci gaba da mu’amala da kamfanonin canjin Kudi

cbn new

Babban bankin Najeriya CBN ya musanta wani labari da ke cewa ya kara wa’adin ci gaba da hulɗa da kamfanonin canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare watau BDC zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, Misis Hakama Sidi Ali, muƙaddasar Daraktan sashen sadarwa a CBN din, ta bayyana waɗannan bayanai a matsayin karya da yaudara, inda ta ce ya kamata a yi watsi da su.

A cewar ta, bankin bai yi wani karin wa’adin da ya wuce wa’adin da aka bayar a baya ba na ranar 3 ga watan Yuni.

Ta kuma bukaci jama’a da ‘yan jarida da kafafen yada labarai da duk masu ruwa da tsaki da su riƙa tantance bayanai kai tsaye daga majiyoyin CBN a hukumance.

Ta ƙara da cewa irin waɗannan majiyoyi sun hada da shafin Internet na CBN da hanyoyin sadarwa da aka ba su izini, kafin a buga ko yaɗa labarai game da Bankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here