A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta gayyaci Manajan Daraktan Kamfanin Kula da Kadarorin gwamnatin tarayya Ahmed Kuru.
An yi wa Kuru tambayoyi kan zargin karkatar da wasu kadarori gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa Ahmed Kuru, wanda har zuwa karfe 9 na daren laraba yana amsa tambayoyi, ana zargin shi da taka rawa wajen sayar da kadarorin gwamnati ga wasu mutane ba bisa ka’ida ba.
An ce ya siyar da kadarorin ga abokansa da ‘yan uwansa da sauran abokan sa na aiki akan farashi mai rahusa.
Wata majiya ta ce: “An gayyaci MD na AMCON ne biyo bayan korafe-korafen da wasu masu cin bashi suka yi wanda aka sayar da kadarorinsu a kan farashi mai ban dariya.
“Jami’an tsaro sun bukaci ya mayar da martani kan zargin da aka kebe masa. A cikin sa’o’i bakwai da suka gabata, ya yi ta yin bayani ga EFCC. Ina tsammanin zai iya kwana tare da mu.”
Da yake amsa tambaya, majiyar ta kara da cewa: Kuru ya musanta zargin da ake masa.









































